Wasu Matasa Sunyi Kone Kone A Dalilin Zuwa Buhari KATSINa Yau
Wasu matasa sun yi jefe-jefe tare da kona tayoyi suna ihun bama yi bama yi bayan shugaban kasa ya kaddamar da gadar Kofar Kaura a Katsina
Wasu matasan da ba a san ko suwanene b sun farmaki jami’an tsaro tare da yin jifa a Katsina jim kadan bayan shugaban kasa Buhari ya bar wurin da ya kaddamar da gadar kasa da Masari ya gina a Katsina.
Kamar yadda majiyar Katsina Daily News ta Leadership ta rawaito, matasan sun zo wurin da suka yi jifar ne bayan shugaban kasa ya kaddamar da gadar ya bar wurin
Wani ganau da abin ya faru a gabansa mai suna Mustapha Muhammad Boss kamar yadda ya sheda wa Leadership, ya ce matasan sun tafo daga wurare daban-daban, suna ihu bama yi bama yi, sannan kuma suka yi jifa ga jami’an tsaron dake wurin tare da kona tayoyi, wanda hakan ya yi sanadiyar dole suka rufe shagunansu da suke kasuwanci a wurin don gudun kaucewa matsala.
Haka kuma wasu bidiyoyi kuma da ake yadawa a kafafen sadarwa, an ga yadda matasan ke jefar kan mai uwa da wabi ga jami’an yan sandan
Daga karshe jami’an tsaro sun kwantar da tarzomar ta hanyar watsa barkonon tsohuwa, inda kawo yanzun komai ya daidaita cikin birnin.
A ziyarar da shugaban kasar ke yi ta kwana biyu a Katsina, a yau ya bude gadar kurde ta Kofar Kaura, tare da kamfanonin shinkafa na Darma Rice da wasu muhimman abubuwa a Katsina, inda ko a gobe ana sa ran shugaban kasar zai bude wasu muhimman ayyuka a Musawa da wasu garuruwa da gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamnatin Rt Hon Aminu Bello Masari ta aiwatar tare da kammalawa.